Hakikanin Asalin Akidar Ta’addanci:
Darwiniyanci da Ta’addanci
GABATARWA
Mutane da yawa sun dauka cewar Charles Darwin ne ya fara kirkiro ka`idar
juyin halitta(theory of evolution) wanda ya rataya akan hujjoji, lura
da gwaje-gwajen kimiyya. Saboda haka, ta wannan fuska, Darwin ba shine
ya kirkiro ba, ballantana ma ka`idar ba`a kafa ta akan hujjojin kimiyya
ba. Ka`idar ta kunshi daukar yanayi (nature) daga imanin mutanen Da akan
falsafar jari-hujja. Duk da cewar dai babu wata hujja ta kimiyya, sabo-
da haka, sun marawa ka`idar baya ne a karkashin sunan falsafar jari-hujja.
Wannan tsantseni ya haifar da annoba iri-iri. Saboda haduwar da yada
akidar Darwin da Falsafar jari-hujja suka bunkasa, da amsar tambayar 'Menene
dan Adam?'ya canza. Mutanen da suka saba fadin:Allah ne ya halicci `yan
Adam, kuma su rayu akan kyawawan dabi`un da ya (Ubangiji) koyar sun fara
canza tunaninsu zuwa'Mutum ya samu ne haka nan, kuma dabba ne wanda ya
ginu da fafutukar rayuwa. 'Lalle zasu biya farashi mai nauyi akan wannan
gagarumar yaudara. Akidu masu kawo rigingimu, irin su wariyar launin fata,
mulkin kama-karya, kwaminisanci dadai sauran akidoji munana wadanda sun
alakantu da wannan yaudara.
Wannan gaba ta tattaunawa zata yi nazari akan annobar da Darwinism ko
akidar Darwin ta jawowa duniya da alakar ta da ta`addanci, daya daga cikin
muhimman matsalolin da suka addabi duniya a zamaninmu.
Karyar Darwin:'Rayuwa Rikici ce'
Darwin ya fitar da wata fahimta daya, lokacin da yake bunkasa ka`idarsa
cewa:
"Bunkasar abubuwa masu rai sun dogara ne akan gwagwarmayar
rayuwa. Mai karfi ya danne mara karfi. Mai rauni kuwa an dammara shi
da zama a haka. "
Darwin yana cewa, akwai dawwamammiyar gwagwarmayar rayuwa da rikici
a yanayin rayuwa. Mai karfi kullum shine a saman mara karfi, kuma wannan
shi zai tabbatar da samuwar cigaba. Sunan da ya sawa littafinsa shine
'The Origin of species by means ofNatural Selection', ko 'The preservation
of Favoured Races in the struggle for Life', ya tabbatar da waccan
magana ko ra`ayi.
Bayan haka, Darwin yayi hasashen wai 'gwagwarmayar rayuwa' za
ta iya shiga cikin jinsin mutum. A da`awarsa, 'zababbun jinsi sune sukai
nasara a wannan gwagwarmaya' zababbun jinsi a wurin Darwin sune turawan
yamma. Afrika da Asiya sune aka bari a baya a wannan gwagwarmayar
rayuwa. Darwin ya cigaba da fadin ra`ayinsa cewar wadannan jinsi da sannu
zasu fadi warwas a gwagwarmayar rayuwa kuma a daina jin duriyarsu:
"A wani lokaci mai zuwa, ba wani mai tsawo kamar
yadda karnuka suka auna ba, wayayyun jinsin mutum zasu kare, kuma su
maye al`umomin Da, a ko`ina a fadin duniya A daidai lokaci guda birran
anthropomorphous. . . babu shakka zasu kare. Tsarar dake tsakanin mutum
da makusantan halittu zai dada fadaduwa, zai shiga tsakanin mutum da
yanayi na wayawa, yadda muke fata, koda caucasian ne, da wasu
nau`in birrai kanana kamar dai yanzu ace tsakanin bakaken mutane ko
Australia da gwaggon biri. "1
Wata bahindiya masaniyar Anthropology, Lalita Vidyarthi tayi bayanin
ka`idar juyin halitta din Darwin ta cusa akidar wariyar launin fata a
cikin zaman takewar kimiyya:
"Shi (Darwin) ka`idarsa ta gwagwarmayar rayuwa ta
samu karbuwa da maraba daga wurin masana kimiyyar zaman takewa na zamanin
nan, kuma suka yarda cewa dan Adam ya cigaba ta duk matakin juyin halitta
wanda ya zama wayewar bature ko farar fata. Daga lokacin da aka kai
kashi na biyun karni na goma sha tara, wariyar launin fata ya samu karbuwa
a matsayin dalili daga mafi rinjayen masana kimiyyar turawan yamma.
2
Inda Darwin yake samo wahayi Ka`idar rashin tausayi na Malthus
Inda Darwin yake samo wahayi a wannan fage shine littafin masanin tattalin
arzikin Birtaniya Thomas Malthus 'An Essay on the principle of population'.
Can da akidarsu mummuna, Malthus ya auna yaga cewa lalle mutane suna karuwa
akai-akai.
A ra`ayinsa, abinda yake hana yawan karuwar mutane shine bala`o`i kamarsu
yaki, fari da yaduwar cuta. A takaice dai, a cikin zancensa mai muni yana
cewa, dole wasu mutane su mutu don wasu su rayu. Rayuwarsu shine ma`ana
'dawwamamman yaki'
A cikin karni na sha tara, ra`ayin Malthus ya samu karbuwa. Ajin farko
na masana turawan yamma sun marawa wannan mugun tunani na sa baya. A cikin
kasidar 'The Nazis Secret Scientific Agenda', muhimmancin
karni na 19 dangane da ra`ayin Malthus akan yawan mutane, an bayyana shi
kamar haka;
"A farkon rabin karni na sha tara, a ko`ina a kasahen
Turai, kusoshin Mulki sun taru don su tattauna akan sabon bincike 'matsalar
yawan jama`a da kuma samar da hanyoyin da za`a aiwatar da ra`ayin Malthus,
da kara yawan adadin nakasar talakawa, maimakon a samar da hanyar
tsaftatuwar talakawa, lallai mu kwadaitar akan kishiyar hakan. Abiranenmu
lallai mu matse hanyoyi, da tura mutane da yawa cikin gidaje, kuma mu
dawo da tabarbarewar halaye. A kasashen mu sai mu gina kauyuka kusa
da kudduddufai, kuma musamman kwadaitar da zama a kwazazzabai da wurare
marasa kyau, " da dai sauransu. 3
Dalilin wannan mummunar akida, wato masu rauni da kuma wadanda suka
fadi a wannan gwagwarmaya za`a kawar dasu saboda haka a yawan da ake samu
akai-akai zai yi daidai kenan. Wannan akida ta 'tursasawa talaka' ta samu
aiwatuwa ne a Birtaniya a karni na 19. Wata doka ta raya masana`antu ta
samu kafuwa inda aka sa yara `yan shekara takwas da tara yin aiki na awa
shida a kullum, a wajen hako kol kuma dubbai sun mutu a sanadiyyar haka,
saboda matsanancin yanayin da suka samu kansu. Miliyoyin mutanen kasar
Birtaniya sun shiga halin kaka-nikayi a dalilin tsarin 'gwagwarmayar rayuwa'
wanda Malthus ya gindaya.
Darwin ya rudu da wannan ra`ayi, kuma ya aiwatar dashi akan sauran yanayin
halittu, kuma ya ambata cewa lallai mai karfi kullum shine mai nasara
a cikin yakinnan na wanzuwa. Haka kuma, yayi da`awar cewa wannan ka`idar
gasgatacciya ce kuma ba zata taba canzuwa ba. Daga nan sai ya gayyato
mutane akan su rabu da addininsu kuma su ki yarda da cewa Allah ne yayi
halitta, kuma su himmatu wajen fito da hujjoji da zasu iya yin karo da
abokan adawa akan gwagwarmayar rayuwa.
Abinda 'Shari`ar daji ta haifar': Fin Karfi
A yayin da Darwiniyanci ya haifar da wariyar launin fata a cikin karni
na 19, sai ya dunkule ya zama akidar da zata iya bunkasa ko farfado da
tsundamar duniya cikin zubar da jini a karni na 20:wanda aka fi sani da
Naziyanci.
Karfin rinjayen Darwin zai iya ganuwa a akidojin `yan Nazi. Idan mutum
yai nazarin wannan akida, wadda Adolf Hitler da Alfred Rosenberg suka
yiwa alkibla, zai fahimci cewa akwai manufar 'zabin halitta', 'zabin ma`abota',
da 'gwagwarmayar rayuwa tsakanin jinsuna', wanda aka maimaita su da yawan
gaske a cikin littafin 'The Origin of Species. 'A yayin da ya sanyawa
littafinsa suna Mein Kamf (Gwagwarmaya ta), Hitler, wanda ya samo wahayinsa
daga akidar Darwin ta gwagwarmayar rayuwa da kuma cewa nasara tana ga
mai karfi. Musamman yayi magana akan wannan gwagwarmaya tsakanin jinsuna,
kamar haka;
"Tarihi zai nuna a daular sabon karni wanda babu
canji ga wannan nasara, wanda zai tabbata a sabon tsarin wariyar launin
fata da yanayi zai wajabta shi. "4
A kamfe na 1933 wanda jam`iyyar Nuremberg tayi, Hitler yai da`awar cewa
"jinsi madaukaki ya shugabantar da kansa akan jinsi makaskanci. . . hakki
wanda muka ganshi a yanayi (nature) kuma wanda muka dauke shi halattaccen
hakki.
"Fadin cewa `yan Nazi sun jawu daga ra`ayin Darwiniyanci hujja ce wadda
kusan dukkanin masana tarihi suka yarda da ita. Masanin tarihi Hickman,
ya bayyana jawuwar Hitler game da ra`ayin Darwiniyanci kamar haka;
"(Hitler) mabiyi ne na gaske mai
yada Juyin halitta. Komai zurfafawa, fadadawa a cikin yarda da akidunsa,
abu ne bayananne cewa (manufar gwagwarmaya ta zama mai muhimmanci ne
saboda). . . littafinsa, Mein Kampf, ya debo akidu da ra`ayoyin ma`abota
evolution, musamman ma wadanda suke karfafa gwagwarmaya, mai karfi shi
yake rayuwa da kawar da raunana don a samar da ingantacciyar rayuwa
ko al`umma. "5
Hitler, wanda ya samar da wannan ra`ayi, ya jefa duniya cikin rigingimu
wanda bata taba gani ba. Kabilu da kungiyoyin siyasa da yawa, kuma musamman
yahudawa, sun sha fama da matsanciyar wahala da kisan gilla a hannun `yan
Nazi, yayi sanadiyyar kisan kiyashi na mutane miliyan (55) hamsin da biyar.
Abinda ya haifar da wannan ta`asa a tarihin duniya shine akidar Darwiniyanci
ta 'gwagwarmayar rayuwa' ko 'struggle for survival' a turance.
Kazamin Hadin Gwiwa: Darwiniyanci da Kwaminisanci
A lokacin da mulkin danniya ke hannun daman akidar Darwiniyanci, a haguna
Kwaminisanci ke biye. Hakika kwaminisanci daya ne daga cikin akidojin
dake kare ka`idar Darwin.
Dangantakar dake tsakanin Darwiniyanci da Kwaminisanci, na komawa ne
ga wadanda suka kafa su. Marx da Engels, sune suka kafa Kwaminisanci,
kuma sun karanta littafin nan na Darwin wato 'The Origin of Species'
a daidai lokacin da ya fito kuma suka gamsu da tsarin maganganun halayyar
jari-hujja. Alakar dake tsakanin Karl Marx da Engels ta nuna cewar sun
fahimci ka`idar Darwin a matsayin abinda ke bada hujjar tarihin yanayin
bawa Kwaminisanci kofa. A littafinsa mai suna 'The Dialectics of Nature',
wanda ya rubuta a sanadiyyar ruduwar Darwin, Engels yayi mutukar yabawa
Darwin, kuma yayi kokarin ba da ta sa gudunmawar akan ka`idar a babin
'The part played by labour in the transition from Ape to Man';
`Yan Kwaminisancin Rasha, wadanda ke bin sawun Marx
da Engels, kamarsu Plekhanov, Lenin, Trotsky da Stalin, dukkaninsu sun
yarda da ka`idar juyin zamanin Darwin(Darwin`s theory of evolution). Plekhanov,
wanda ake ganin shine ya dasa harsashen Kwaminisancin Rasha yana daukar
Marxism a matsayin 'Darwiniyanci a aikace a ilmin zaman tare'.
6
Trotsky yace; "Binciken Darwin shine babbar
nasara a duk fadin fagen nazarin gabar halittu. "7
Ilmin Darwiniyanci yana da rawa mai yawa da ya taka
wajen haifar da kwaminisanci. Misali, masana tarihi sun tabbatar cewa
Stalin mai addini ne a samartakarsa, amma ya daina addini saboda
littattafan Darwin. 8
. Mao, wanda ya kafa tsarin mulkin kwaminisanci a China
kuma ya kashe miliyoyin mutane, ya fada a bainar jama`a cewa 'an
kafa kwaminisancin China ne akan tafarkin Darwin da ka`idar evolution.
' 9
Masanin tarihin Harvard University James Reeve Pusey
yayi cikakken bayani da ya danganci Darwiniyanci akan Mao da Kwaminisancin
China a littafinsa na bincike mai suna 'China and Charles Darwin'. 10
A takaice ai, babu wata kafa dake raba tsakanin ka`idar evolution da
kwaminisanci. Ka`idar tazo da cewar dukkan wani abu mai rai ya wanzu ne
haka nan, kuma suka kawo hujjojinsu na shaci fadi da sunan kimiyya don
tabbatar da addinin maguzanci. Kwaminisanci kuwa, akida ce wadda ta kulla
alakar ta da Darwiniyanci. Bayan haka, ka`idar ta cigaba da cewa cigaban
yanayi na iya yiwuwa ta hanyar gwagwarmayar rayuwa (struggle for survival)
da marawa akidar 'dialectics' baya wadda jigo ce a kwaminisanci.
Idan muka tuna akidar kwaminisanci ta 'dialectical conflict'wato rikicin
wariyar harshe wadda tayi sanadiyyar mutuwar mutum sama da miliyan dari
da ashirin (a cikin karni na ashirin, 20th century), zamu iya
fahimtar irin annobar daDarwiniyanci ya gayyatowa duniya.
Darwiniyanci da Ta`addanci
Kamar yadda muka gani a baya, Darwiniyanci shine mabubbugar akidu masu
yawa wadanda suke tattare da rigingimun da suka haifarwa dan Adam annoba
a karni na 20. Haka kuma, kamar dai wadannan akidu, shima Darwiniyanci
ko akidar babu Allah, ya bayyana 'daidaitacciyar fahimta' da 'tsari'wanda
zai iya jan hankalin ra`ayoyiiri-iri a duniya. Manufar da take karkashin
wannan fahimta da kuma tsarin shine 'yakar wadanda basa cikinmu'.
Zamu iya fayyace wannan kamar haka; Akwai akidu, ra`ayoyin duniya, da
falsafa iri-iri. Kowannensu na kallon dan uwansa a dayan biyun wannan
hanyoyi:
1) Zasu iya girmama bayyanar wadanda basa tare dasu da kokarin kulla
alaka ta sulhu ko tattaunawa, wato suyi amfani da tsari na mutuntaka;
ko
2) Zasu iya zabar su yaki wasu, da kuma kokarin samun damar raunana
su, ma`ana dai, suyi amfani da halayya irin ta dabbobi.
Abin tsoron da muke kira ta`addanci ba wani abu bane illa bayanin nan
na ra`ayi na biyu.
Idan muka kalli bambancin dake tsakanin ra`ayoyin biyu, zamu ga cewa
salon da Darwiniyanci ya dauka na cewa wai "mutum wata dabba ce
mai dabi`ar fada" kawai an rudi mutane ne ta karfin tuwo. Daidaikun
mutane da jama`arsu wadanda suka zabi wannan hanya ta rigingimu, watakila
basu taba sanin wani abu mai suna Darwiniyanci da akidunsa ba. Amma a
karshe, sun zo sun yarda da ra`ayin Darwiniyanci. Abinda ya jawo suka
yarda da ingancinsa shine, taken Darwiniyanci kamar, 'mai karfi shi yake
rayuwa a wannan duniya', 'babban kifi shi yake hadiye kanana', yaki dabi`a
ce', da kuma 'mutum na cigaba ne ta hanyar jangwalo yaki'. Ku jefar da
Darwiniyanci can gafa, domin ba komai bane illa fankon da babu tsinke
a ciki.
Hakika, idan aka jefar da Darwiniyanci, to, babu wata falsafar rikici
da zata rage. Addinai ukun da mafi yawan mutane suka yi imani dasu, Musulunchi,
Kiristanci, da Yahudanci, sun kyamaci rikici. Dukkaninsu na fatan su kawowa
duniya zaman lafiya ne, da kyamar kashe mutanen da basu jiba kuma basu
gani ba, cutar dasu da azabtar dasu. Rigingimu da tayar da tarzoma sun
karya tsarin dabi`un da Ubangiji ya shiryawa dan Adam, kuma ababan kyama.
Sai dai, Darwiniyanci ya gabatar dasu a matsayin yanayi mai afkuwa, nagaskiya
kuma babu makawa sai sun wanzu.
Saboda haka, idan wasu mutane suka aikata ta`addanci ta hanyar fakewa
da addinin Musulunchi, Kiristanci da Yahudanci, za ka iya tabbatarwa ba
Musulmai, kiristoci ko Yahudawa bane. Mabiya addinin Darwin ne. Suna fakewa
a inuwar addini da muminai ne.
Kuma dalili shine suna aikata abinda addini ya hana, ba don komai ba
sai don su bakanta addini a idon mutane Saboda haka, tushen ta`addancin
da ya cika wannan duniya tamu bashi da alaka da daya daga cikin saukakkun
addinai, sai dai maguzanci ne, kuma fassara maguzanci a zamaninmu shine:'Darwiniyanci'
da Jari-hujja.
MUSULUNCHI BA SHINE YA HAIFAR DA TA`ADDANCI BA,
SAI DAI HANYAR WARWARE SHI
Mutanen da suke cewa suna aiki da sunan addini na iya rashin fahimtar
addininsu ko su aikata shi abisa kuskure. Saboda haka, kuskure ne samo
wani abu daga wurin wadannan mutanen akan abinda ya shafi addini. Hanya
mafi kyawun fahimtar addinin Musulunchi shine ta asali mafi tsarki.
Hanya mafi tsarki a Musulunchi shine Alkur`ani: kuma samfurin kyawawan
dabi`u kur`ani shine Musulunchi-ya sha bamban da duk wani yanayin da ya
darsu a zukatan wasu turawan yamma. An saukar da kur`ani ne akan kyawawan
dabi`u, soyayya, tausayi, jinkai, kaskantar da kai, kwazo, juriya da zaman
lafiya, kuma Musulmin da yake rayuwa akan wannan tafarki, lallai ya tsarkaku,
ga hangen nesa, juriya, gaskiya da rikon amana. Wadanda suke kewaye dashi
na amun kauna, girmamawa, zaman lafiya da fahimtar zaman takewa ta rayuwa
tare dashi.
Musulunchi addinin zaman lafiya ne kwanciyar hankali
Kalmar ISLAM tana daidai da ma`anar "zaman lafiya" a larabce. Musulunchi
saukakken addini ne da ya zowa rayuwar dan Adam cike da zaman lafiya da
kwanciyar arziki, wanda rahama da jinkan Ubangiji ya bayyana a duniya.
Ubangiji yayi kira ga mutane suyi koyi da kyawawan dabi`un da kur`ani
ya koyar a matsayin abin koyi daga rahama, jinkai, juriya da zaman lafiya
wanda duniya za ta dandana. A suratul Baqara, aya ta 208, an bada wannan
umarni kamar haka;
" Yaku wadanda suka yi imani! Ku shiga cikin Musulunchi
gaba daya;kuma kada ku bi zambiyoyin Shaidan;lalle ne shi a gareku makiyi
ne, bayyananne. "
Kamar yadda muka gani a wannan aya, mutane zasu iya samun rayuwa mai
walwala kadai idan sun shiga Musulunchi kuma suka rayu akan koyarwar Alkur`ani.
Allah ya hana zalunci
Ubangiji ya umarci dan Adam da ya guji barna, kafirci, rashin mutunci,
kangarewa, kisan kai, da zubar da jini. Wadanda suka sabawa wannan umarni
to lallai suna kan tafarkin Shaidan, kamar yadda aka bayyana a ayarda
ta gabata, kuma aka bayyana shi da cewa abin haramtawa ne daga wurin Ubangiji.
Daga cikin ayoyi masu yawa da suka yi bayani akan haka, ga guda biyu;
"wadanda suka warware alkawarin Allah daga bayan
kulla shi, kumasuna yanke abinda Allah yayi umarni dashi domin a sadar
dashi kuma suna barna a cikin kasa. Wadancan suna da wata la`ana, kuma
suna da munin gida. "(suratul ra`ad:aya ta 25)
"A Kuma ka nema, a cikin abinda Allah ya baka
gidan lahira, kuma kada ka manta da rabonka daga duniya. Kuma ka kyautata
kamar yadda Allah ya kyautata zuwa gareka, kada ka nemi barna a cikin
kasa. lalle ne Allah ba ya son barna"(suratul qasas:aya ta 77)
Kamar yadda zamu iya gani, Ubagiji yayi hani ga duk wani nau`i na zalunci
a addinin musulunchi, har da ta`addanci da hada tarzoma, kuma ya la`anci
masu aikata hakan. Musulmi shine zai iya arawa duniya kyau ya kuma ingantata.
Musulunchi Na kare Iko da `yancin Magana.
Musulunchi addini ne da yake tabbatar da `yancin rayuwa, fahimta da
tunani. Yayi hani ga tashin hankali, rigingimu, rudani, da zato kai har
da mugun tunani da ka iya yiwa wani illa. Musulunchi ba wai kawai ya hana
ta`addanci ko tarzoma ba, kai duk kankantar abinda zai iya cutarwa akan
wani dan Adam an hana shi.
"Babu tilastawa a cikin addini, hakika
shiriya ta bayyana daga bata; saboda haka wanda ya kafirta da Daguta
kuma yayi imani da Allah, to, hakika yayi riko ga igiya amintacciya,
babu yankewa a gareta. Kuma Allah mai ji ne, masani. "(Suratul baqara:
aya ta 256).
"Ka isar musu da gargadi, domin gargadi ne
kawai gareka, baka da ikon tursasa su akan suyi imani. "(Suratul ghashiya:
22)
Tilastawa mutum yayi imani da addini ko aikatashi, ya sabawa hikima
da manufar musulunchi saboda wajibi ne ace imani ya karbu ta hanyar sakakkiyar
iko da zabin zuciya. Koda yake, musulmi ya iya kwadaitar da wani akan
bin koyarwar Alkur`ani, amma ba tare da tilastawa ba. Haka kuma, ba `a
son jan hankalin mutum izuwa addini ta hanyar bashi wani abin amfani na
duniya.
Amma bari mu kwatanta abin a kishiyance. Misali, kasar da ake matsawa
mutane da dokar kasa don su yi addini. Wannan kasa ko al`umma ta sabawa
addinin musulunchi saboda imani da bauta suna kima idan har an
fuskantar dasu ga Allah. Idan dai har akwai wani tsari dake tilastawa
mutane su yi imani da bauta, to mutane zasu zama suna biyayya ne don tsoron
wannan tsari kawai. Abinda yake karbabbe ta fuskar addini shine, addini
yana aiwatuwa ne a cikin al`ummar da take da `yancin rayuwa, kuma a aikata
shi da nufin yardar Ubangiji.
Allah ya haram ta kisan mutanen da basujiba , basu ganiba
. Kamar yadda Alkur`ani ya bayyana, daya daga cikin manyan zunubai shine
kashe mutumin da bai yi wani laifi ba.
"Daga sababin wannan, Muka rubuta akan Bani
Isra`ila cewa, lalle ne wanda ya kashe rai ba da wani rai ba, ko barna
a cikin kasa, to kamar ya kashe mutane duka ne, kuma wanda ya raya rai,
to, kamar ya rayar da mutane ne gaba daya. Kuma lalle ne, hakika, ManzanninMu
sunje musu da hujjoji bayyanannu, sannan kuma lalle ne, masu yawa daga
gare su, a bayan wannan, hakika, masu barna ne a cikin kasa. "(suratul
ma`ida:aya ta 32);
"kuma wadanda ba su kiran wani Ubangiji tare
da Allah, kuma ba su kashe rai wanda Allah Ya haramta face da hakki,
kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka. "(suratul furqan:aya
ta 68).
Kamar yadda muka gani a wadannan ayoyi na sama, wadanda suka kashe mutanen
da ba su jiba ba su gani ba, to ana tsoratar dasu da azaba mai radadi.
Ubangiji ya bayyana cewa kashe mutum, girmansa kamar kashe mutane ne baki
dayansu. Duk wanda yake girmama dokokin Allah ba zai cutar da wani ba,
ballantana yayi sanadiyyar kashe miliyoyin mutanen da basu jiba basu gani
ba. Wadanda suke tunanin kubuta daga hukunci anan duniya, ba zasu taba
kubuta daga tambayar da zasu amsa a gaban Ubangiji gobe kiyama ba. Saboda
haka, mummunan da suka san cewar zasu bada bayani gaban mahalicci bayan
mutuwarsu, zasu yi taka-tsantsan wajen kula da dokokin da Ubangiji ya
shimfida.
Allah Ya Umarci Mummunai da su Zama Masu Rahama
da Jinkai.
A wannan aya, an bayyana dabi`un musulmi da cewa;
"Sannan kuma ya kasance daga wadanda suka yi imani,
kuma suka yiwa juna wasiyya da yin hakuri, kuma suka yiwa juna wasiyya
da tausayi. Wadannan ne ma`abota albarka. "(suratul balad:aya ta 17-18).
Kamar yadda muka gani a wannan aya, daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci
a kyawawan dabi`un da Ubangiji ya saukarwa bayinsa ko sun samu gafara
da jinkai da samun aljanna shine su "kwadaitar da junansu da yin
rahama."
Kamar yadda Alkur`ani ya siffanta musulunci da cewa addini ne na kowane
zamani, mai wayar da kai da samar da cigaba. Musulmi shine wanda yafi
kowa son zaman lafiya, mai iya juriya da yanayin zamantakewar siyasa,
mai riko da al`adun addini, mai gaskiya kuma wayayye, masani akan rayuwa,
kimiyya da wayewar zamani.
Musulmi masani ne ga kyawawan dabi`un da alkur`ani ya koyar, yana mu`amala
da kowa tare da soyayya irin wadda musulmi yake bukata. Yana girmama dukkan
wata hikima, kuma yana kimanta ilmi. Kuma shi mai kawo sulhu ko hadin
kai ta kowace fuska, tare da kawar da duk wani rikici ko sabani. A cikin
al`ummar da ake samun irin wadannan mutane, za`a samu cigaban rayuwa,
farin ciki da walwala, adalci, tsaro, yawan albarka fiye da kowace kasa
mai cigaba a wannan duniya ta yau.
Ubangiji Ya Umarci Kawaici da Gafara
Suratul A`raf, aya ta 199, wadda tace "ku yawaita gafara", na nuna cewar
kawaici da gafara suna daya daga cikin ginshikan addinin musulunci.
Idan muka kalli tarihin musulunci, zamu gani a bayyane yadda musulmi
suka kafa wadannan muhimman dabi`u daga koyarwar alkur`ani a rayuwarsu
ta yau da kullum. A kowane lokaci a rayuwarsu, musulmi sun rushe dukkanin
haramtattun ayyuka kuma sun tabbatar da zaman lafiya. A bangaren da ya
shafi addini, harshe da al`adu, sun saukaka rayuwa inda mabanbantan mutane
suka rayu a inuwar `yanci da zaman lafiya, kuma suka bawa wadanda suke
karkashinsu damar yin ilmi, tara dukiya da samun matsayi na shugabanci.
Wannan yana daya daga muhimman dalilan da ya fadada daular Ottoman kuma
ta dade karnuka masu yawa, domin wannan shine tsarin rayuwartìyawa, kuma
su samu damar walwalar rayuwa da al`adunsu ba tare da wani tsangwama ba.
Hakika, kawaicin musulmi, idan aka aiwatar kamar yadda Alkur`ani yayi
umarni, zai kawowa duniya zaman lafiya da karuwar arziki. Alkur`ani ya
bayyana irin wannan dabi`a da cewa;
" Kuma kyautatawa bata daidaita da munanawa. Ka tun
kude da yake mafi kyau, sai gashi wanda akwai kiyayya a tsakaninka da
tsakaninsa, kamar dai shi majibincin ne masoyi. "(suratul fussilat:
aya ta 34)
Kammalawa
Dukkanin wadannan suna nuna kyawawan dabi`un da addinin musulunchi ya
gabatarwa dan Adam a matsayin abinda zai kawo zaman lafiya, farin ciki
da adalci ga duniya. Abubuwan da suke faruwa na rashin jin dadi a duniyarmu
ta yau a karkashin sunan addinin musulunci, "Ta`addanci", ya fita daga
tsarin koyarwar Alkur'ani, aiki ne na jahilai, mutane masu ketare iyaka,
masu laifi wadanda ba ruwansu da addini. Hanyar da za'a yaki wadannan
mutane da suke fakewa da musulunci, shine umartar mutane don suyi aiki
da hakikanin koyarwar addinin musulunci.
A takaice dai, addinin musulunci da koyarwar Alkur'ani basa goyon bayan
ta'addanci da 'yan ta'adda sai dai suna kawo hanyar da duniya zata kubuta
daga ta'addanci. |